TASIRIN YAWAN KARANTA RUBUTATTUN WASANNIN KWAIKWAYO A KAN QWAZON XALIBAN MANYAN MAKARANTUN SAKANDAREN JIHAR KADUNA A FANIN NAHAWUN HAUSA

Authors

  • Ahmed MUSA1, L. J. MAGAYAQI1 and B. D. USMAN2 Ahmadu Bello University, Zaria

Abstract

Wannan bincike mai taken “Tasirin Yawan Karanta Qagaggun Labarai a Kan Qwazon Xaliban
Manyan Makarantun Sakandaren Jihar Kaduna a Fanin Nahawun Hausa” An gabatar da
manufofinsa guda huxu tare da tambayoyi huxu daga manufofin da kuma hasashen bincike
su ma guda huxu. Binciken ya mayar da hankali wajen gano tasirin amfani da dabarar yawan
karanta qagaggun labarai wajen inganta qwazon xalibai a nahawun Hausa. Akwai jimillar
manyan makarantun Sakandare 340 a shiyyoyin ilimi 12 da suke da xalibai ‘yan aji biyu (SS
II) su 27,779 a Jihar Kaduna inda aka gudanar da binciken. An yi amfani da samfurin zaɓin
canki-canka aka zaɓo makarantu biyu da Ɗalibai 360 ‘yan aji biyu (SS II). Watau, daga
makarntar G.S.S Zariya a matsayin makarantar gwaji da kuma G.G.S.S Alhuda-huda wadda ta
ke ta lura. An gudanar da binciken ne ta amfani da tsarin gwaji, inda aka raba xalibai zuwa
rukuni na gwaji da rukuni na lura. An yi amfani da jarabawar gwaji a farko da kuma ƙarshe
da koyarwa ta hanyar yawan karanta ƙagaggun labarai domin tattara sakamakon binciken.
Sakamakon binciken bayan yin amfani da ƙididdigar ma’aunin gwajin-t da kuma ma’aunin
p, ya nuna cewa akwai tasiri da fifiko sosai a tsakanin Ɗaliban da aka koyar da su Nahawun
Hausa ta hanyar yawan karanta ƙagaggun labarai da waɗanda ba a koyar da su ba ta wannan
hanyar ta fuskar iya sanin kalmomi da sanin ma’anar suna a nahawu da sanin kalmomin
aikatau da sanin wakilin suna a nahawun Hausa. Domin kuwa an samu 0.00 daga ƙididdigar
ma’aunin -p a dukkan hasashen binciken guda huɗu wanda bai kai 0.05 ba da aka ɗora
hasashen binciken. Hakan ne ya sa aka yi watsi da hasashen. Saboda haka binciken ke ba da
shawarar cewa malamai da hukumomin tsara manhaja da su rungumi koyar da yawan
karanta ƙagaggun labarai a matsayin wata sabuwar dabara ko hanyar koyarwa. Sannan
kuma hukumomin Ilimi su himmatu sosai wajen ɗaukar ƙwararrun malaman Hausa da ba su
horo domin inganta harkar koyarwa.

Author Biography

Ahmed MUSA1, L. J. MAGAYAQI1 and B. D. USMAN2, Ahmadu Bello University, Zaria

Ahmed MUSA1, L. J. MAGAYAQI1 and B. D. USMAN2
1DEPARTMENT OF ARTS SOCIAL SCIENCE EDUCATION, FACULY OF EDUCATION. AHMADU BELLO UNIV. ZARIA
ahmedmtaba10@gmaik.com:08062688007,lubabatujibomagayaki@gmail.com070625
83474
Tsakure
DA
2DEPARTMENT OF NIGERIAN LANGUAGES AND LINGUISTIC KADUNA STATE UNIVERSITY, KADUNA
baladogara1111@gmail.com:08068139485

Downloads

Published

2026-10-15